– An sace wani babban Jami’in Soja
a Garin Legas
– A jiya ne dai aka nemi wani Laftanan Soji aka rasa
– Babu
mamaki masu garkuwa da mutane suka yi gaba da shi
A jiya Litinin ne aka nemi
wani babban Jami’in Sojan Najeriya aka rasa a Garin Legas. Wannan abu dai ya
faru ne a Yankin FESTAC da ke Garin Legas da yammacin jiya. Ana zargi masu
garkuwa da mutane ne suka sace Sojan.
Duk da cewa kwanan nan
Gwamna Ambode na Jihar ya shigar da dokar harbe duk wanda aka kama yana satar
mutane da alamu wasu ba su koyi hankali ba tukun. Wasu bata-gari ne dai suka
kai hari ga Rundunar Sojin yayin da suke wucewa, bayan nan aka nemi wani Soja
aka rasa.
Yanzu haka an shiga neman
wannan Soja da aka bayyana da Laftana Diya a Yankin na Unguwar FESTAC, Sojoji
da sauran Jami’ai sin hargitsa wurin da harbe-harbe da sauran cikin bacin ran
‘dan uwan su da suka nema suka rasa.
Kwanaki ne kuma Mutanen
Garin Agatu na Jihar Benuwe su ka tsokano tsuliyar dodo idan har ba ayi wasa
ba, don kuwa sun kashe wani Sojan Najeriya kwanan a wata hatsaniya da aka yi
tsakanin mutanen Garin da Jami’an tsaro. Sai dai sun nemi a yefa masu kuskuren
na su.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment