Tuesday, February 28, 2017

Tsufa ba zai sa in ajiye aiki ba-Mugabe


– Shugaban kasar Zimbabwe yace yawan shekaru ba za su sa ya ajiye mulki ba


– Shugaba Mugabe ya cika shekaru 93 a Duniya


– Mugabe yace sam bai da niyyar sauka daga mulki





Shugaban Kasar Zimbabwe Robert Mugabe yace yawan shekaru ba za su ya sa sauka daga kujerar mulki ba. Mugabe dai ya cika shekaru 93 da haihuwa a Duniya ya kuma sam bai da niyyar sauka daga mulki.

Robert Mugabe ne dai shugaban kasar da ya fi kowane dadewa a Duniya ya kuma yi shekaru 37 yana mulkin kasar Zimbabwe. Mugabe dai yayi bikin cika shekara 93 a Duniya inda ya bayyana cikin bakin tabaron sa.




Shugaba Mugabe yace bai ga ranar da zai sauka ba bayan ya dade yana shugabanci. Mugabe yace idan har zai sauka daga mulki ba zai yi kokarin kakabawa Jam’iyyar wani dan takara ba da zai yi mulki. 

Kwanaki Wani Fasto mai suna Patrick Mugadaza ya bayyana cewa shugaban na kasar Zimbabwe, Robert Mugabe zai rasu a cikin watan Oktoban wannan shekarar, ko da ya sanar da hakan sai ‘Yan Sanda suka kama shi. A Kasar Zimbabwe bai hallata kace shugaba Mugabe zai mutu.



[NAIJ Hausa]




No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...