Friday, February 24, 2017

Wani mugun ciwo ya dawo Najeriya



Wani mugun ciwo ya kara dawowa Najeriya



‘Lassa’ mugun cutar nan da aka sani ta dawo gari yanzu haka har ta aika wasu bayin Allah Lahira. Kamar dai yadda aka sani dabbobi irin su bera ne ke kawo zazzabin na Lassa.

Kamar yadda muka samu labari daga jaridar Daily Trust, wannan mugun cuta ta dawo Garin Bauchi har kuma tayi sanadiyar mutuwar mutane 4. Kwamishinar lafiya ta Jihar bauchi Dakta Halima Mukaddas ta bayyanawa manema labarai wannan a yau.

Dakta Halima tace an samu bullowar cutar ne a Garuruwan Alkeri da Ganjuwa. Kwanakin baya dai wannan zazzabi na lassa ya bullo gari inda yayi sanadiyar rashin rayukan mutane kusan 2 a Bauchi. An dai gargadi Jama’a su guji bera wanda shi ke yada kwayar cutar.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...