Monday, February 27, 2017

Abubuwan da Osinbajo yayi bayan tafiyar Buhari




Tun tafiyar shugaba Muhammadu Buhari kawo yanzu mukaddashin shugaban kasar Yemi Osinbajo ya dauki matakai da ayyuka da dama a kasar. A wani nazari da muka yi, mun jero manya daga ciki




Yanzu haka dai Farfesa Osinbajo ke rike da Najeriya ya kuma yi ayyuka tafiyar shugaba Buhari na a-zo-a-gani. Kadan daga ciki su ne sauyi da aka gani a tsare-tsaren harkar kudin kasar daga CBN. Farfesa Osinbajo kuma ya shiga lungunan Neja-Delta domin kwantar da rikicin da ke Yankin.

Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya saki kudin wasu manyan kwangiloli a Kaduna da Legas wancan makon bayan taron Majalisar FEC. Haka kuma Shugaban rikon kwaryar ya ci burin gyara tattalin arzikin Najeriya ta hanyar saukake harkar kasuwanci a kasar cikin watanni biyu.

Tun hawan sa dai ya nada Kwamiti domin ya ji dalilin da ya sa farashin abinci ya tashi a Najeriya. Farfesa Osinbajo ya kuma gana da shugabannin Majalisa ba sau daya ba, ba sau biyu ba a game da harkar kasafin kudin wannan shekarar.

Osinbajo ya kuma rattaba hannu a wasu kudirori da Majalisar ta aiko masa yayin da kuma yayi mursisi yayi watsi da wasu kudirorin tare da bayyana dalilan sa. Har a kasar waje dai ana ta kawo ziyara ga shugaban kasar na rikon karya inda shi ma ya taka har kasar Gambia wajen nadin sabon shugaba Adama Barrow.


[NAIJ Hausa] 



No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...