– Shugaban kasa na rikon-kwarya Osinbajo yayi doguwar waya da Buhari
– Osinbajo ya sanar da Buhari cewa ana zanga-zanga
– Buhari na cikin koshin lafiya
Inji Mataimakin Sa
Mukaddashin
shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kara tabbatar da cewa Muhammadu Buhari na nan
cikin koshin lafiya. Osinbajo yace kuma Buhari zai dawo Najeriya yana kammala
gwajin da yake yi a asibiti.
Osinbaji
yayi doguwar waya da Muhammadu Buhari ya kuma bayyanawa ‘Yan Jaridan da ke
Fadar shugaban kasar abin da suka tattauna a wayar. Osinbajo yace sun tattauna
ne game da tattalin arzikin kasa da kuma batun kasafi da Buhari.
Mukaddashin
shugaban kasa Osinbajo yace ya kuma fadawa Buhari cewa ana zanga-zanga a kasar
inda mutane ke kuka musamman game da tattalin arziki. Sannan kuma dai Osinbajo
yayi watsi da rade-radin cewa ana nema a tursasa ya sauka daga kan kujera, yace
babu wanda ya isa.
A
jiya ne aka gudanar zanga-zanga ga Gwamnatin Buhari saboda halin da ake ciki a Kasar a halin
yanzu. Wani Babban Jigo Jam’iyyar APC
mai mulki Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayi kira ga ‘Yan Najeriyan da su kara
hakuri.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment