– Tsohon shugaban kasa Olusegun
Obasanjo ya bayyana ranar da ba zai taba mantawa da ita ba
– Tsohon shugaba Marigayi Janar Abacha ya kama Obasanjo da laifin zai
kifar da Gwamnati
– An
yankewa Obasanjo hukuncin mai tsanani
Tsohon shugaban kasar
Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana ranar da ta fi masa kowace takaici a
Duniya. Olusegun Obasanjo dai ya mulki kasar nan a mulkin soji da ma farar hula
na sama da shekaru 10.
Cif Obasanjo yace ranar da
ba zai taba mantawa da ita ba ita ce ranar da tsohon shugaba Janar Abacha ya
kama sa aka yanke masa hukuncin kisa wanda daga baya ya koma daurin shekaru 30
har ya kai shekara 15 a gidan yari. An zargi Obasanjo da yunkurin yin juyin
mulki ga Gwamnatin Sojin Janar Sani Abacha.
Obasanjo yayi wannan bayani
ne a jiya yayin da ake bikin ranar soyayya ta Duniya watau ‘Valentine’ a gidan
sa da ke Ogun. Cif Obasanjo yace ba zai taba mantawa da wannan rana ba.
Obasanjo dai bai wuce shekaru 3 a daure ba Abacha ya rasu, yana fitowa kuma ya
zama shugaban kasa.
Janar Sani Abacha ya sa an kama Shehu 'Yaradua tare da Obasanjo bisa zargin juyin mulki, wanda shi a karshe ya mutu a gidan yari.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment