– Wasu ‘Yan iskan Garin sun kai wa Gwamna Mimiko hari
– ‘Yan
iskan sun kai harin ne ga tawagar Gwamnan
– Sun
dai hana Mai Girma Gwamnan zuwa Majalisa
Wasu ‘yan iskan Gari sun kai
hari ga tawagar motocin Gwamnan Jihar Ondo Olusegun Mimiko. Wadannan ‘Yan iska
dai sun yi barna ga motoci biyu da ke cikin tawagar.
Wannan abu dai ya faru ne
yayin da Gwamnan ke kokarin zuwa Majalisar Jihar domin ya bayyana kasafin kudin
wannan shekarar. Mazauna Yankin dai sun san yadda suka yi, suka hana Gwamnan da
tawagar sa wucewa.
Hukumar dillacin labarai na
Kasa watau NAN tace rikicin yayi kamari, don haka dole Gwamnan ya fasa zuwa
inda yayi niyya. A karshe dai mutane da dama sun samu rauni don aran-gamar da
suka yi da Jami’an tsaro. Sai dai mutanen sun ce zanga-zangar su ke yi ba tada
rikici ba, su na mai kokawa da halin ‘Yan Sandan.
A can Jihar Kaduna kuma,
Hukumar ‘Yan Sanda ta samu nasarar damke wasu daga cikin masu hannu a rikicin
Kudancin Kaduna. ‘Yan Sanda dai sun kama mutane 17 da manyan makamai guda 29.
Za a gurfanar da wadannan mutane a Gaban Kotu.
No comments:
Post a Comment