– Ma’aikatan
Gwamnati sun koka da halin da ake ciki a Najeriya
– Ana fama da masifan rashin kudi
– Shugaba Buhari yana yaki da cin hanci da rashawa a
Najeriya
A wani bincike da wata
Jarida tayi an gano cewa Ma’aikatan Najeriya sun koka da irin halin da ake ciki
na rashin kudi a Najeriya a wannan mulki na shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Abin dai har ya kai ga manyan motoci hannun Ma’aikata amma babu kudin zuba masu
mai.
Ma’aikatan Najeriya dai sun
saba cuwa-cuwa watau ha’inci to yanzu ta kai kowa yana dogara ne da dan
albashin sa. Hakan dai ta sa Jama’a na ta cire ‘Ya ‘yan su daga manyan
Makarantu masu mugun tsada. Ana dai ganin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari
ya hana mutane damar da suke samu a da.
A lokacin baya Najeriya ta
samu makudan kudi daga bangaren mai, hakan ya sa aka yi ta facaka, sai dai fa
yanzu abubuwa sun canza tun zuwan Muhammadu Buhari. Yanzu haka an maida asusun
kudin Kasar zuwa biai daya watau TSA wanda wannan ya kawo sauyi kwarai da
gaske.
Wadanda suka saba barna da
kudi sun shiga cikin wani hali da ba su saba ba, wasu ma dai na da wasu mutanen
dabam a karkashin su. Yayin da kudin sata yayi wuya, sai kowa ya zama
kaffa-kaffa. Ko ya za a kare da Yaki da rashawar da wannan Gwamnati ta dauko?
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment