–
Mutane sun fara tofa albarkacin bakin su game da maganganun Sarki Sanusi II
– Sarkin
Kano yace za a hana talaka yawan aure a kasar sa
–
Wannan maganar ta jawo ce-ce-ku-ce a Gari
Kalamai da kudirin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II sun
jawo ce-ce-ku-ce a Gari yanzu haka a cikin mata. Mai Martaba Muhammadu Sanusi
II yace za a hana talaka tubus kara auren mata a kasar sa.
A wata hira da Hukumar dillacin labarai na kasa watau
NAN tayi da wasu mata a Maiduguri, wasu sun bayyana cewa hakan abu ne mai kyau
yayin da wasu matan kuma suka ce gaba daya bai dace a kawo irin wannan doka
ba.
A wani bincike da Jaridar Daily Trust tayi wasu matan
sun nuna cewa sun yi na’am da Sarki suka nemi kuma a mara masa baya, wasu matan
dai sun ce hakan na iya kawo matsala ga matan da ke neman mazaje ido rufe.
Sarkin dai yace za a hana wadanda talauci ya masu
katutu aure barkatai wanda a karshe suke gaza kula da ‘ya ‘yan su, Sarkin yace
wannan ke kawo ‘ya ‘ya a Gari wadanda suke zama ciwon kai ga al’umma. Wasu dai
sun ce ko ya za iya da tarin ‘yan matan da ke Gari?
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment