Monday, February 27, 2017

Ya aka yi Darajar Naira ke tashi?


– A cikin ‘yan kwanakin nan dai Naira ta tashi


– Naira tayi tashin da ba ta taba yin irin sa ba


Ko ta ya aka cin ma wannan?





Hakar babban bankin Najeriya na CBN ta fara ci wa ruwa don kuwa har abubuwa sun fara yin kyau. Kwanan nan ne dai babban bankin kasar watau CBN ya sauya tsare-tsaren sa na harkar kudin kasar bayan Mukaddashin shugaban kasa da kuma Ministan kudi sun fito sun yi magana cewa ya kamata a canza tsari.

A lokacin da aka zauna dai ana sa ran Dalar na iya zarce N600 idan ba ayi wasa ba, hakan ta sa dole aka sake sabon lale. Bayan kwanaki kadan dai sai ga CBN da sababbin manufofi wanda suka taimaka yanzu Dalar tana ta kara yin kasa.

Ko da ma can dai kudin kasar wajen Najeriya yana ta kara habaka bayan da aka hana shigo da abubuwan da ba su da wani tasiri daga kasar waje irin su farantin kwangiri da tsinken sakace. Yanzu dai asusun Najeriya na kudin kasar waje ya zarce Dala Biliyan $30. Wannan ya ba CBN damar zubo dalolin wanda da ‘yan kasuwa sun boye su.

An dai kuma dai yi katari rikici a Yankin Neja-Delta ya fara raguwa kuma gangar man Najeriya yayi tsada a kasuwa, wannan ya sa Najeriyar ta samu wasu ‘yan rara. Ko shin ya za a daure da haka?


[NAIJ Hausa] 




1 comment:

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...