–
Ministan harkokin mata tace sai su fi makonni 5 ba tare da wutan lantarki ba
– Aisha
Jummai Alhassan ta bayyana haka ne a gaban majalisa
–
Rashin wuta dai ya zama ruwan dare a Najeriya
Da alamu dai rashin wutan lantarki ya zama ruwan-dare
a Najeriya, a jiya ne Ministar harkokin mata Aisha Jummai Alhassan tace har
Ma’aikatar ta sai a shafe fiye da wata day aba tare da kiftawar wuta ba.
Mama Taraba kamar yadda aka san ta, tace rashin wuta
ne ya hana ta kawo takardun da ake bukata wajen tattaunawa da kuma tsefe
kasafin ma’aikatar na wannan shekarar. Aisha Alhassan tace rashin wuta ne ya
addabe su a Ma’aikatar wanda a wani lokaci sai a kusa makonni 6 babu wutar
lantarki.
Ministar tace dole ita da Sakataren Ma’aikatar suka
hada kudi daga aljihun su suka saye man da aka yi amfani da shi a Injin
janareto. Ministar tace rashin wuta ne dai ya hana ta zuwa ta kare kasafin
ma’aikatar ta a Majalisa, tace ba za a kara yin hakan ba.
Haka dai kwanaki aka dauke wuta yayin da ake tantance Jakadun kasar a cikin Majalisar Dattawan Kasar. Rashin wuta dai ya zama ruwan-dare.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment