– Wani
Saurayi ya auri wanda ta yi jika da shi
– An dai ce ita soyayya ba
ruwan ta
– Dan
shekara 28 ya auri tsohuwa ‘yar 82
Da yake shi ‘so’ ba gani
yake yi ba, ga dai wani matashi na dan shekara 28 ya buge da auren wanda ta
girme sa da shekaru 54 a Duniya. Wannan abu dai ya faru ne a can kasar
Indonesia.
Ko da yake dangin juna ba su
so wannan aure ba amma aikin gama ya gama tun da masoyan suka ce sun ji sun
gani. Kwanan baya ne wani matashi mai aikin kwadago Sofian Laho Dandel ya shiga
soyayya da wata tsohuwa Martha mai shekaru fiye da 80 a Indonesia.
Bisa dukkanin alamu dai
Duniyar nan ta zo karshe don kuwa kwanaki muka samu wani labari da ba mu taba
jin irin sa ba shi ma. A Kasar Zambia wani saurayi ne ya auri mahaifiyar sa
bayan uban sa ya rasu.
No comments:
Post a Comment