– Hukumar
kwallon kafa na Duniya FIFA za ta cigaba da hukunta Chris Giwa
– Dama can Chris Giwa da wasu suna cikin masu laifi
– Chris Giwa na rikici da Shugaban
kwallo NFF na Najeriya
Kungiyar
FIFA ta kwallon kafa na Duniya za ta cigaba da hukunta wasu Jami’an kwallon
kafar Najeriya watau NFF. FIFA tace har yanzu ba ta yafewa Chris Giwa da sauran
Jami’an Najeriya da ta samu da laifi ba.
Kungiyar
FIFA ta Duniya ta kama Chris Giwa da wasu da rikicin shugabancin kujerarar NFF
na Najeriya a baya. Sauran Jami’an da aka hukunta sun hada da Muazu Suleiman,
Johnson Effiong, Fema Sani da Yahaya Adama.
Idan
dai ba a manta ba Chris Giwa ya kalubalanci shugaban kwallon kafan Najeriya NFF
watau Amaju Pinnick yace sam shine shugaba ba wani ba. Bayan nan ne FIFA ta
Duniya ta takawa Giwa da mukarraban sa burki, aka kuma hana su shiga kowace
irin harka ta kwallon kafa a Duniya.
No comments:
Post a Comment