– A rana irin ta yau aka kashe Janar Murtala a shekarar 1976
– Su
Laftana Kanar Dimka suka kashe Murtala a cikin mota a Legas
– Janar Obasanjo ya karbi mulki a bayan rasuwar shugaban
kasar
Janar
Murtala ya karbi mulkin kasar nan ba tare da an kashe ko dan tsako ba a Ranar
29 ga Watan Yulin 1975. A wancan lokaci shugaban kasa Yakubu Gowon ba ya kasar.
A lokacin yakin basasa Murtala yayi namijin kokari lokacin yana rike da babban
bataliya ta biyu.
A
dan lokacin da Murtala yayi mulki don kuwa bai wuce kwanaki 200 ba rak. Ya
sallami ma’aikata da dama domin gyara harkar kasar har da tarin Sojoji. Murtala
ya fara shirin mikawa farar hula mulki bayan wani lokaci da kuma maida Birnin
Tarayya zuwa Garin Abuja tare da yi wa tsarin kasar garambawul. Ko da ya rasu
kafin nan, hakan kuwa aka yi.
Bayan
an kashe Janar Murtala dai, Janar Obasanjo ne ya karbi mulkin. Janar Obasanjo
ya harbe wadanda suka kashe Janar Murtala Muhammad har lahira. A wancan lokaci Muhammadu
Buhari ya rike Gwamnan tsohuwar Jihar Borno.
A
yayin da matar Janar din ta ke jiran sakon farin ciki watau ana shirin bikin
ranar Valentine na masoya, sai
kwatsam kawai ta ji labarin mutuwar Mijin na ta. An dai birne Janar Muratala a
Garin Kano. Masana sun ce da ace yayi tsawon rai da Najeriya ta ga sauyin
gaske.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment