Sunday, February 5, 2017

A bar tuna-baya, Karuwa ta zama Minista


Wai a bar tuna-baya Inji Hausawa Mahaukaci ya zama Sarki


– A Kasar Zimbabwe wata mai-zaman kan ta ta zama Ministar yada labarai


Ministar ta roki a bar tuna baya





Wata Minista a Kasar Zimbabwe ta nemi ‘Yan Kasar su bar tuna lokacin baya, Ministar dai ta taba zaman kan-ta a baya, tace amma yanzu ai komai ya wuce, kuma kyaun ta a dai bar tuna baya.

Minista Kampamba Mulenga ta yada labarai a Kasar Zimbabwe tace abin da za ayi la’akari da shi yanzu shine aikin ta a matsayin Ministan yada labarai. Ministar tace yanzu ta canza ta kuma ajiye wancan aiki a gefe.

Ministar tayi wannan magana ne inda ta ke nuna takaicin ta da wasu da ke kiran ta da sunan da aka san ta a da. Kampamba Mulenga ta cewa Mutanen Kasar yanzu ta canza ya kamata kuma al’umma su ba ta girman ta. Kafin ta zama Minista a Gwamnati dai kamar yadda Daily Post ta rahoto kowa ya san ta a matsayin mai zaman kan ta.

A farkon wannan Watan tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya gabatar da jawabi a gaban Majalisar Amurka inda aka gayyace sa domin yayi magana game da matsalolin Najeriya musamman rikicin addini da sauran su.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...