– Hukumar
EFCC ta karbe gidan tsohon Gwamna Isa Yuguda
– Wata Kotu ce ta ba EFCC damar karbe kayan tsohon
Gwamna na Bauchi
– Ana binciken Yuguda da laifin satan dukiyar Jama’a
Hukumar EFCC mai yaki da cin
hanci da rashawa ta karbe wasu kaya na tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Isa Yuguda.
Wannan ya biyo bayan wani babban Kotu da ke Abuja ta ba Hukumar damar hakan.
Yanzu haka dai Hukumar ta
EFCC ta karbe gidan tsohon Gwamna Yuguda da ke Unguwar GRA na Bauchi. Wani
Jami’in Hukumar EFCC yace za a rike gidan ne na wani dan lokaci kafin a kammala
bincike.
Ana zargin tsohon Gwamnan da
laifin satar kudin Jama’a da wuce gona da iri lokacin yana kan kujera. Alkali
J. Tsohon na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta ba Hukumar EFCC damar karbe
kayan tsohon Gwamnan a wancan makon.
No comments:
Post a Comment