Wednesday, February 22, 2017

'Yan Najeriya sun ga azaba a kasar waje

– Mutanen Najeriya da suka dawo daga kasar Libya sun ce ba irin wahalar da ba su gani ba a can


Jiya aka dawo da wasu ‘yan kasar nan daga Libiya


– ‘Yan Najeriya sun bayyana irin hazan da su ka ji a kasar waje





A jiya Talata ne jirgi ya sauka daga kasar Libiya dauke da ‘Yan Najeriya a filin jirgi na Murtala Muhammad da ke Legas. ‘Yan Najeriyan dai sun bayyana irin yadda suka samu rayuwa a inda suka je, suka ce babu irin bala’in da ba su gani ba.

‘Yan Najeriyan sun ce sun ga azaba a kasar Libiya, suka ce asali ma dai yaudarar su aka yi su ka tafi kasar tun farko, yanzu haka dai wadansu mutane 171 daga cikin mutanen sun ji ba Sarki sai Allah sun tsero Inji Hukumar Dillacin labarai na kasa watau NAN.




Wata mata mai suna Gift Peters tace ita dai yaudarar ta aka yi, aka ce mata za a kai ta kasar Italiya, sai ga su sun buge a kasar Libya da ke Arewacin Afrika. Wannan mata tana hawaye tace har bawali sun sham wani lokaci kuma a nana masu karfe mai zafi saboda azaba.

Mutanen dai sun yi da na-sani suka komai lalacewa gida ya fi daji. Shugaban kasa dai yayi alkawarin za a taimaka ma wadanda aka dauka daga kasashen. 


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...