Thursday, February 23, 2017

Buhari yayi magana da mutanen Kano


– Manyan malaman Kano sun yi shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a


– Sheikh Daurawa yace shugaba Buhari na bukatar addu’a


Gwamna Ganduje yayi magana da shugaba Buhari





Kusan duk wani babban malami yana cikin gidan gwamnatin Jihar Kano jiya inda aka yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a. Malaman sun yi wa shugaban addu’ar karin lafiya ya samu ya cigaba da mulkin kasar nan.

Manyan malami irin su Malam Aminu Daurawa, Sheikh Isiyaka Rabi’u, Sheikh Muhammad Nasir Adam, Sheikh Adam Suleiman da sauran Shehunnai suka halarci gangamin inji Jaridar Vanguard. An dai ta karatun Kur’ani domin shugaba Buhari ya samu waraka.

Shugaban Hisbah Sheikh Daurawa yace shugaban kasar na bukatar lafiya domin ya cigaba da tafiyar da al’amurar kasar nan tare da goyon bayan Jama’a. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi magana kai-tsaye da shugaban kasar inda ya bayyana yadda Jama'a ke ta masa addu'a, shugaba Buhari yayi matukar godiya ga mutanen a wayar tarho.





[NAIJ Hausa]






No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...