Thursday, February 2, 2017

Babban dan wasa ya ajiye kwallo




Babban Dan wasan nan na Ingila Frank Lampard ya ajiye wasan kwallon kafa bayan yayi shekara da shekaru ana gwabzawa da shi. Lampard dai ya dauki fiye da shekaru 20 yana taka leda a Kasar Ingila da kuma Amurka.
Lampard ya fara bugawa Chelsea tun a shekarar 2001 bayan ya baro Kungiyar West Ham, sai da ya kai har shekaru fiye da goma a Kungiyar. Frank Lampard ya kuma bugawa Kasar sa ta Ingila kwallo na kusan shekaru 15.
Dan wasa Lampard ya kafa tarihi inda ya fi kowa cin kwallaye a Chelsea, Lampard duk da dan wasan tsakiya ne ya ci wa Chelsea kwallayen da ba a taba samun irin su ba. Lampard ya zurawa Chelsea kwallaye 211; wanda ya fi na duk wanda ya taba bugawa Kulob din.
Lampard ya sanar ta Facebook cewa daga yanzu ya aijye tamula yana kuma mai alfahari da sunan da yayi. Lampard ya ci kwallaye kimanin 300 a fadin wasan rayuwar sa. Da alamu Lampard zai dawo bangaren horas da ‘Yan wasa. Lampard yayi ritaya yana da shekara 38.

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...