– Likitoci sun shiga yajin-aikin a Asibitin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya
– Yajin aikin ya shafi sauran Malaman Asibiti
– Ma’aikatan sun ce babu ranar dawowa
Jaridar
Daily Trust ta rahoto cewa Malaman Asibitin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya sun
shiga wani yajin aiki jiya. Kwanan ne dai aka sake bude Asibitin bayan an
kaddamar da wasu gina-gine an kuma canza masa suna.
Ma’aikatan
dai wanda suka hada da Likitoci da sauran Malaman Asibiti sun tafi yajin ne a
jiya wanda kuma suka ce babu ranar dawowa har sai Hukuma ta duba kukan su.
Ma’aikatan dai sun ce Hukumar Jami’ar ta gaza biya masu bukatun da suka yi
yarjejeniya.
Shugabannin
Kungiyoyin Ma’aikatan Asibitin guda hudu dai suka rattaba hannu a kan takardar
da ke sanar da cewa Ma’aikatan Asibitin za su koma yajin aikin su. Wani ya bayyana
mana cewa ya je Asibitin amma ba a aiki dole ta sa ya dawo gida. Har yanzu dai
Jami’ar ba tace uffan ba.
Haka
dai kwanaki Likitocin Asibitin koyan-aiki na Jami’ar dai ta Ahmadu Bello suka
shiga yajin-aiki na din-din-din. Kungiyar Likitocin Asibitin da ke Shika, sun
shiga yajin aikin ne bayan an gaza biya masu bukatun su.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment