Friday, February 24, 2017

Za a samu husufin rana a Najeriya


– Za a samu husufin rana a Najeriya


– Masu nazari sun ce Ranar Lahadi wannan abu zai faru


Sai dai an ce abin ba zai yi kamari ba




Masana masu hange da binciken Duniya sun bayyana cewa za a samu husufin rana a sassan kasar nan a Ranar Lahadi. Ko da yake dai masanan sun ce abin ba wani mai kamarin gaske bane.

Kungiyar bincike game da cigaban sararai na kasa watau NASRDA tace wannan abu zai faru ne karshen makon nan kamar yadda ta fadawa hukumar dillacin labarai na kasa NAN jiya a Birnin Abuja.

Masanan sun ce wannan abu zai faru ne a ko ina na fadin kasar. Hasken ranar za ta fi raguwa ne kuma a Yankin kudancin kasar irin su Fatakwal, Kalaba da Garin Uyo. Inda kuma abin ba zai yi wani tasiri ba shi ne Yankin Arewacin kasar musamman Jihar Kebbi.

Wannan abu dai zai faru ne da yammaci akasari daga bayan karfe 4 zuwa karfe 6. Ba dai yau aka fara samun husufi a Najeriya ba, kuma baa bin tada hankali bane. A irin wannan yanayi mutane kan fito suyi ta addu’a.


[NAIJ Hausa]


No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...