Thursday, February 9, 2017

Dan wasan Jamus Phillip Lahm zai ajiye kwallo


Tauraron dan wasan Kasar Jamus Phillip Lahm ya ajiye kwallo


– Dan wasa ya ajiye kwallo bayan ya kafa tarihi


Lahm bai taba samun jan kati ba





Babban Dan wasa kuma Kyaftin din Kasar Jamus da kuma Kungiyar Bayern Munich Philip Lahm ya bayyana cewa daga karshen wannan shekarar zai daina taka leda. Lahm yana da shekaru 33 a yanzu haka.

Bayan dai fiye da shekaru 20 ana murzawa dan wasan bayan yace ya gaji hakanan, zai koma gida ya huta. Lahm ya bugawa Bayern wasanni sama da 500 sannan kuma ya bugawa kasar Jamus wasa sama da 100 har ta kai ya rike kambu.

Lahm dai ya ci kyaututtuka da kofuna da dama a Duniya. An kuma nemi ya zauna a Kulob din a cigaba da damawa da shi, amma yace sam akwai gyara tukun. Tun da Lahm yake kwallo a Duniya dai bai taba karban jan kati ba.





[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...