– Ko ka taba
ganin Diyar shugaba Muhammadu
Buhari Hannan
– Hannan ita ce ‘yar autar
Baba Buhari
– Hannan Buhari tana sha’awar
daukar hotuna
Wasu hotunan
diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari sun bayyana a shafin gizo. An dai ga ‘yar
autar shugaban kasan a wani hoto rike da ‘kemera’ abin daukar hoto. Hannan din
dai mai shekara 18 tana da sha’awar daukar hoto.
Hannan Muhammadu
Buhari ta dauro hoton ne a shafin ta a cikin bakin launi. Sai dai masu bin
Diyar shugaban kasar a yanar gizo sun tofa albarkacin bakin su a game da hoton.
Jama’a dai suna cewa Diyar shugaban kasar tana da dan-karen kyau.
Sai dai wani
daga cikin masu-bin Diyar shugaban kasar ya ba ta shawarar cewa bai dace ta saka
bakin hoto ba, watau kamar ana wani makoki. Ana dai ta rade-radin cewa shugaba
Buhari na kwance a Landan bai da lafiya.
Hannan da kemarar ta
[NAIJ Hausa]
Allah Ya ba baba lafia. Hausawa Na cewa kowa da sana'ar da ta karbe shi... Hannan Allah YA ba da sa'a.
ReplyDelete