Me
ka sani a game da Dujal?
Ya
tabbata dai a hadisai na Manzon Allah SAW cewa Dujjal zai bayyana a can karshen
Duniya. Ko wanene Dujjal? Yaushe zai zo? Ya za ayi da shi?
Dujjal dai zai zo a karshen Duniya ya kuma kawo fitina babba
kamar yadda Annabi SAW yayi bayani. Dujjal zai do ido guda yayin da dayan yake
kuma a shafe, sannan a gaban goshin sa an rubuta ‘kafir’ da larabci. Haka
Dujjal zai keta Duniya cikin ‘yan kwanaki kadan.
Dujjal dai zai rika tafiya da Jama’a wadanda suka yi
imani da shi, wadanda suka kafirce masa kuma yayi masu barazanar azaba. Kai har
dai na kabari bai tsira ba daga wannan mugun halitta. Saboda haka ne Manzon
Allah yayi umarni da haddace da karanta Suratul Kahfi a cikin Al-Qur’ani.
Dujjal dai yana daga cikin alamomin karshe na tashin
kiyama, tare da Mahadi da kuma Annabi Isa wanda zai dawo nan gaba kamar yadda
Hadisai suka nuna. Zai zagaye Duniya kaf ban da kasar Makka mai tsarki.
Wata rana ne dai Annabi Isa AS bayan ya dawo Duniya zai
isa wani wuri tare da sauran Musulmai sai ya iske Dujjal a wani Gari mai suna
Lud kusa da Garin Tel-Aviv sai ya jefa masa mashi ya kashe sa.
Allah yayi mana gab-da-katar daga sharrin Dujjal. Ameen.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment