Sunday, February 5, 2017

Shugaban Kasa Buhari na shirin dawowa


 Shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin dawowa Najeriya


– Buhari ya tafi hutu Kasar Birtaniya tun watan jiya


Zuwa gobe Shugaban kasa Buhari zai shiga Ofis






Idan ba a manta ba Shugaba Muhammadu Buhari ya bar Najeriya ne a Ranar 19 ga Watan Junairu inda ya tafi hutu Kasar Birtaniya. To da alamu dai jirgin Shugaban kasar ya fara shirin tashi don kuwa lokacin dawowan sa gida yayi.

Shugaba Buhari ya nemi Majalisa ta san da tafiyar sa zuwa hutun inda ya kuma nemi Mataimakin sa Yemi Osinbajo ya zama Mukaddashi har sai ya dawo. Zuwa gobe dai ake sa ran cewa Shugaba Buhari zai shiga Ofis.




A lokacin da ba ya nan an ta yada jita-jita iri-iri cewa Shugaba Muhammadu Buhari yam utu a can. Har sai da ta kai an fito da hotunan sa inda yake shakatawa kana wasu su ka yarda yana raye. Kungiyar nan ta Izalatul Bidi’a wa Iqamatus Sunnah ta Kasa ta soki masu kirawa shugaba Buhari mutuwa. Kungiyar ta ce kowa idan lokaci yayi zai mutu.

Wata Kungiya mai suna NYCN ta matasan Najeriya dai za ta shirya taron gangami na mutane 1500 domin murnar dawowan Shugaba Buhari.



{NAIJ Hausa}




No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...