Monday, February 27, 2017

Bola Tinubu zai tsaya takara?





Wani babban jigo a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yace yana iya tsayawa takarar shugaban kasar nan, ko da yake dai babu wanda ya san gobe.

Tsohon Gwamnan Legas, Bola Ahmed Tinubu yace zai iya neman kujerar shugaban kasa nan gaba. Tinubu yayi wannan magana ne a wajen bikin rantsar da sabon Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akerodolu.

A wata hirar bidiyo da Tinubu yayi da Sahara Reporters ya bayyana cewa ba zai ce a’a ba game da takarar shugaban kasa, Bola Tinubu yace shugabanci na kasa kamar bauta ne da yi wa kasa hidima.

Bola Tinubu yace yana iya takara nan gaba don babu abin da ya hana sa, sai dai yace hakan na iya danganta da yanayi na siyasa da sauran su. Tinubu yace ko shugaba Muhammadu Buhari sai bayan ya cire rai ne ya samu mulki.



[NAIJ Hausa]









No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...