– A
cikin ‘yan kwanakin nan dai Naira ta tashi
–
Naira tayi tashin da ba ta taba yin irin sa ba
–
Ko ta ya aka cin ma wannan?
Hakar babban bankin Najeriya na
CBN ta fara ci wa ruwa don kuwa har abubuwa sun fara yin kyau. Kwanan nan ne
dai babban bankin kasar watau CBN ya sauya tsare-tsaren sa na harkar kudin
kasar bayan Mukaddashin shugaban kasa da kuma Ministan kudi sun fito sun yi
magana cewa ya kamata a canza tsari.
A lokacin da aka zauna dai ana
sa ran Dalar na iya zarce N600 idan ba ayi wasa ba, hakan ta sa dole aka sake
sabon lale. Bayan kwanaki kadan dai sai ga CBN da sababbin manufofi wanda suka
taimaka yanzu Dalar tana ta kara yin kasa.
Ko da ma can dai kudin kasar
wajen Najeriya yana ta kara habaka bayan da aka hana shigo da abubuwan da ba su
da wani tasiri daga kasar waje irin su farantin kwangiri da tsinken sakace.
Yanzu dai asusun Najeriya na kudin kasar waje ya zarce Dala Biliyan $30. Wannan
ya ba CBN damar zubo dalolin wanda da ‘yan kasuwa sun boye su.
An dai kuma dai yi katari
rikici a Yankin Neja-Delta ya fara raguwa kuma gangar man Najeriya yayi tsada a
kasuwa, wannan ya sa Najeriyar ta samu wasu ‘yan rara. Ko shin ya za a daure da
haka?
[NAIJ Hausa]
mardin
ReplyDeleteerzincan
kars
antep
çorum
4JG