– Sarkin
Kano Sanusi II yace za a hana talaka yawan aure a kasar sa
–Malamin
nan na Izala Sheikh Jingir yace idan aka yi haka ba a yi daidai ba
– Sheikh
Jingir yace Al-Kur’ani ya bada damar auren mata 4
Shugaban Majalisar
malamai na Kungiyar nan ta Jama’atul Izalatul bidi’a wa iqamatus sunnah watau
JIBWIS yace sam bai dace Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II yayi maganar cewa za a hana talaka tubus kara auren mata a
kasar sa ba.
Malamin yace hakan ba daidai bane don kuwa Al-Kur’ani
ya ba maza damar auren mata har 4. Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana haka ne
yayin da yake magana da manema labarai a Garin Jos. Shehin ya nemi Sarkin ya
gana da Malamai domin shawo kan matsalolin aure.
Jingir yace a irin wannan lokaci da ake da zaurawa da
dama, auren su zai kara wahala idan har aka kafa wannan doka. Malamin ya kuma
nemi Jama’a su ji tsoron Allah a gidajen auren su. Sarkin ya bayyana yadda ya
rika samun koke-koke daga mata game da yadda tsofaffin mazajen su ke watsi da
kula da ‘ya ‘yan da suka haifa yace aikin sa ne ya dauki mataki.
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II dai yace wannan mataki ya zama dole dalilin yadda iyaye maza ke watsi da tarbiyyar 'ya 'yan na su.
[NAIJ Hausa]
Allah Ya qarawa Sarki lafia. Shi Jingir Sai yanxu zai ce Sarki ya gana da malamai, Ai kamata yayi wannan maganar da yayi ya aika masa da sako (personal). Duk maSu sukar maganar Sarki bin son zuciya da kungiyanci ya haha su nutsuwa ya haha su fahimtar asalin jawabin Sarki. Allah Ya ganar da su.
ReplyDelete