Wednesday, February 15, 2017

An kusa daina dauke wuta a Najeriya


Kasar Amurka za ta saka kudi wajen harkar wutan Najeriya


Amurka na shirin kashe dala biliyan 1 a Najeriya domin ganin an samu wuta


Idan har hakan ta yiwu za a daina dauke wutar lantarki a Kasar




Kasar Amurka na shirin kashe makudan kudi domin ganin Najeriya ta samu wutar lantarki tsayayye. Amurka dai za ta cigaba da kokari a kan harkar wutar lantarki a Nahiyar Afrika domin ganin an fita daga duhu.

Amurka na shirin saka kudi har dala biliyan guda a Najeriya domin gyara wutar lantarki. Tun ba yau ba dai Kasar ta saba taimakawa Najeriya. Asali ma dai an kashe makudan kudi daga shekarar 1999 zuwa yau amma har yanzu babu tsayayyen wutar lantarki a Najeriya.

Kamar yadda Jaridar The Nation ta rahoto, Mista Andrew Herscowitz wanda shi ne mai kula da Kwangilar Power Africa ya bayyana haka a wani taron karawa juna sani da aka yi a Abuja. Idan har aka samu karin mega watta 30, 000 tabbas za a daina dauke wuta a Najeriya.




[NAIJ Hausa]

1 comment:

  1. Shu Shugaban kasar amuruka da ya ce baya san bakakin mutanen, me ya hada shi da taimaka masu? Ya rike taimakon shi

    ReplyDelete

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...