HUDUBAR
JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA
Me muke nema a Duniya?-Daga
Bakin Imam Sheikh S. S Abubakar
A’udhu BilLahi minasshaidan
Ar-Rajim, BismilLahir Rahman Ar-Raheem,
Dukkan Godiya sun tabbata ga
Allah SWT, muna rokon gafarar Sa da samun yardar Sa. Godiya da yabo sun tabbata
gare shi Madaukakin Sarki. Muna shaidawa lallai babu abin bauta da gaskiya face
Allah SWT, Shi kadai yake, babu abokin tarayya a gare Sa. Muna shaidawa lallai
Shugaban mu, Annabi Muhammad SAW Bawan Allah ne kuma Manzon Sa ne.
Bayan Haka:
Ya dace mu rika tambayar
kawunan mu bayan lokaci wai ‘shin me ‘Dan Adam yake nema a doron kasa?’ Sau da
yawa sai kaji mutum yace yana son rayuwa ta farin ciki a cikin Duniya na dukiya
masu dinbin yawa. Sai ka ga mutum yana ta kokari wajen samun natsuwa da hutu a
cikin rayuwar Duniya. Da yawa su na neman morewa a cikin rayuwa, ko mecece
morewar? Dankareren gida cike da masu hidima da motoci da sutura na alfahari da
abinci mai dadi, sune abin morewar? Mafi yawanci dai abin da ‘Dan Adam yake
nema kenan a rayuwa ko da bai furta hakan ba. Ko da yake ba wannan ne matsalar
ba, sai dai hanyar da Jama’a ke bi wajen samun wannan rayuwar ita ce suke
bacewa, su rika lalube cikin rudun su, suna masu dimaucewa, suna fadi-tashi.
Irin wannan al’amari dai bai dace ya samu ‘Dan uwa Musulmi ba. Ya kai Mumuni
mai tsoron Allah wanda ya tasiran tu da Imani, ai lallai kai ne ke cikin jin
dadi idan har ka samu imani. Duk wanda yayi abin da ya dace da imani shi ne
wanda yake jin dadin Duniya kuma zai rabota a Lahira. Hanya ta hakika guda daya
da za ta kai mutum ga abin da yake buri shi ne Addinin Musulunci. Face wannan
Addini babu abin da zai kai ka ga wannan buri, bari ganin irin abin da mutane
suke ciki na dukiya, wannan duk ba shi bane rayuwa na farin ciki. A kullum ka
riko rokon Allah SWT ya yarda da kai, kuma Allah SWT ya so ka. Saboda haka abin
da ya kamata shi ne mu ji tsoron Allah SWT mu guji saba maSa. Don mun ga mutane
da yawan dukiya ko matsayi na mukami ko duk wani daukaka, ko ka ga har wani
yana jin dadi yana tare da masu matsayi, ya samu yardar manya; ‘Ai mun yi waya
da Alhaji yace yana Landan, daga nan zai wuce Faransa…’ Wani dai shi ko wannan
ya ishesa kasaita, sai a ga kamar wadannan mutane sun samu wata Daula ta
Duniya, wannan ba ita ce alama ta yardar Allah ba; Allah SWT yana ba da Duniya
ga wadanda yake so da kuma wanda ba ya so. Da ace darajar wannan Duniya ta kai
na fiffiken sauro a wajen Allah, da kafiri bai samu ruwan da zai kurba ba. Shi
yasa ma Malamai ke cewa Allah SAW ya hana Manzon Sa, ba-dadin Sa Duniyar duk da
cewa shi ne zababben zababbu wanda ya fi kowa martaba da daraja cikin halittu.
Tare da haka Allah ya zabawa Annabi SAW rayuwa ta talauci da kuma yunwa, Allah
ya fada maSa cewa: ‘Lahira ta fiye maka wannan Duniya.’ Da Duniya tana da
daraja da babu wanda zai fi samun babban rabo irin Annabi SAW kamar yadda Allah
mai girma zai fifita Sa SAW a Ranar lahira; Manzon Allah SAW zai kai matsayi na
Mukamal-Mahmud wanda babu wanda ya
isa ya kai wannan matsayi a Kiyama. Sau da yawa Sahabbai sun ga Manzon Allah SAW
ya daura duwatsu a kan cikin sa saboda yunwa, ko da Manzon Allah ya bar Duniya
abincin da ya rage a gidan sa kankani ne a cikin wani ‘dan karamin mazubi;
wanda dai Allah ya sa masa albarka. Annabi SAW ya rasu ya bar sulken yakin sa a
hannun wani Bayahude jingina inda aka ba sa abinci, sai bayan Manzo ya bar
Duniya aka karbo wannan sulke na Sa. Idan har da wadata ta isa wani abu, da wa
ya fi cancanta da ita? To amma kuma ka da mutane su dauka abin da ake so shine
mutum ya zauna ba tare da nema ba. A’a mutum ya nema, amma fa ka rika tunawa da
rayuwar Manzon Allah SAW kuma ka godewa Allah, sannan ka yi amfani da abin da
ka samu wajen abin da Allah yake so. Yana daga cikin rafkana idan har Allah ya
shimfidawa mutum Duniya ya kasance mai sabon Allah. Ka da ya zama kamar Kafirai
wanda an gaggauto masu duk wani jin dadin su a cikin wannan Duniya, bai kamata
Musulmi ya zama mai irin wannan dabi’ar ba ta maras rabo a Lahira. Manzon Allah
SAW ya kira wannan da istidraji, duk
wanda Allah yayi wa wannan mugun kamu to ba zai kufce ba. Mutum zai kasance
yana ta sabon Allah yayin da yake ta kara samun ni’imar Ubangiji, sannu dai
Ubangiji zai damke sa ba-zata. Saboda haka samun ni’imomi ba sa nuna cewa Allah
yana son mutum, kai dai ka cigaba da aikata abin da Allah yake so, sai Ya so
ka. Yana daga cikin siffofin wadanda Allah ya yarda da su, ka ga bawa ya
kaskantar da kan sa ga Ubangiji tare da biyayya da jin tsoron Sa. Yana kuma
daga ciki ka samu mutum mai yawan tuba da kuma mu’umala na gari da sauran bayi
tare da tsarkaka daga ayyukan assha. Haka kuma yana daga cikin halin wadanda
Allah yake so ka ga mutum yana hakuri da juriya wajen biyayya ga Allah da kuma
gujewa saba masa tare da hakuri ga abubuwan da su ka same sa yana mai dogaro da
Allah SWT shi kadai. Haka kuma wadannan mutane shirye suke da yin gwagwarmaya
domin Allah. Sai dai duk wadannan ba su yiwuwa sai mutum yayi riko da sababi.
Ba zai yiwu don mutum yayi dogaro da Allah ba kurum ya koma Masallaci yayi ta
zikiri ba tare da ya fita ya nemi abinci ba. Dole sai mutum ya nemi ko iri na
gona yayi shuka idan an yi ruwa, sai ya dogara da Allah. Dole fa duk abin da za
muyi ya zama addini ya yarda da shi kamar yadda Al-Kur’ani ya fada mana; da ace
Jama’a za su yi imani su ji tsoron Allah sai Ubangiji ya bude masu hanyoyi na
albarkatu ta sama da kasa, sai dai Jama’a da dama suka karyata haka, aka kuma
damke su.
Allah ka ba mu fahimtar
Addini tare da zama lafiya. Allah ya karba mana ya tseratar da mu daga wuta.
Allah Ya Sa albarka cikin aikin mu tare da dadin tsira ga Annabin Mu da Iyalan
sa da wadanda suka yi imani da Shi zuwa Ranar karshe.
Allah ka taimaki kasar mu ka
taimaki shugabannin mu. Allah ka taimaki mai son gaskiya ka taimake sa ka kuma
ba sa lafiya. Ya Allah don kudarar Ka da iradar Ka, Ka ba shugaban Kasar mu lafiya
ka maido mana da shi lafiya ya cigaba da abin da yake yi na alheri. Ameen.
Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga
Masallacin I.T.N-Zaria.
Twitter: @Ya_waliyyi