Wednesday, March 1, 2017

Izala ba ta yarda da yunkurin Sarkin Kano ba


– Sarkin Kano Sanusi II yace za a hana talaka yawan aure a kasar sa


–Malamin nan na Izala Sheikh Jingir yace idan aka yi haka ba a yi daidai ba


– Sheikh Jingir yace Al-Kur’ani ya bada damar auren mata 4





Shugaban Majalisar malamai na Kungiyar nan ta Jama’atul Izalatul bidi’a wa iqamatus sunnah watau JIBWIS yace sam bai dace Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II yayi maganar cewa za a hana talaka tubus kara auren mata a kasar sa ba.

Malamin yace hakan ba daidai bane don kuwa Al-Kur’ani ya ba maza damar auren mata har 4. Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana haka ne yayin da yake magana da manema labarai a Garin Jos. Shehin ya nemi Sarkin ya gana da Malamai domin shawo kan matsalolin aure.




Jingir yace a irin wannan lokaci da ake da zaurawa da dama, auren su zai kara wahala idan har aka kafa wannan doka. Malamin ya kuma nemi Jama’a su ji tsoron Allah a gidajen auren su. Sarkin ya bayyana yadda ya rika samun koke-koke daga mata game da yadda tsofaffin mazajen su ke watsi da kula da ‘ya ‘yan da suka haifa yace aikin sa ne ya dauki mataki. 

Babban malamin Duniya mai fatawa Sheikh Ismail Menk shi kuwa ya goyi bayan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a game da maganar. Babban Shehin yace ko da cewa aure Sunnah ne mai karfi, amma ko Manzon Allah SAW cewa yayi wanda yake da hali yayi, wanda kuma ba sa da shi sai ya hakura, ina kuma maganar karawa.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II dai yace wannan mataki ya zama dole dalilin yadda iyaye maza ke watsi da tarbiyyar 'ya 'yan na su.



[NAIJ Hausa]

1 comment:

  1. Allah Ya qarawa Sarki lafia. Shi Jingir Sai yanxu zai ce Sarki ya gana da malamai, Ai kamata yayi wannan maganar da yayi ya aika masa da sako (personal). Duk maSu sukar maganar Sarki bin son zuciya da kungiyanci ya haha su nutsuwa ya haha su fahimtar asalin jawabin Sarki. Allah Ya ganar da su.

    ReplyDelete

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...