Friday, March 10, 2017

Yadda Shugaba Buhari ya dawo gida



Shugaba Buhari yayi magana





A jiya ne muka samu labarin cewa shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari zai dawo gida Yau Jumu’a. Shugaba Muhammadu Buhari dai ya dauki kusan kwanaki 50 a Landan

A yau ne shugaba Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya da asuba. Shugaban kasar ya iso filin jirgin sama na Kaduna a Jirgin shugaban kasa na Air force kimanin karfe 4:00 na safiya. Mataimakin Gwamnan Jihar Bala Bentex suka tarbe sa.




Bayan nan ne shugaban kasan ya karasa Birnin Tarayya Abuja a wani dan karamin jirgi, A nan dai Mukaddashin shugaban kasa da sauran kusoshin Gwamnati wanda sun dade suna jiran sa. An ga Farfesa Osinbajo da mai ba shugaban kasa shawara game da harkar tsaro Manjo-Janar Munguno suna ta tattaunawa.

Bayan lokaci kadan sai ga jirgin shugaban kasar nan ya dura, Jami’ai kuma suka zagaye say a fito. Shugaba Buhari ya fara gaisawa da Mataimakin sa Farfesa Osinnajo sannan ya gaisa da Abba Kyari da kuma Gwamnan Zamfara da Ministan Abuja, sannan ya gaisa da sauran manyan Jami’ai.



Shugaba Buhari ya gaisa da Femi Adesina kenan sai wani Dan Jarida ya tambaye sa ko ya jikin sa. Shugaba Buhari ya fada masa cewa ai ga shi nan yana ganin sa. Nan shugaban kasar ya shiga motar sa ta Marsandi S550 zuwa Fadar Aso Rock.




No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...