Tuesday, March 7, 2017

Asirin sanannen Fasto ya tonu


Asiri ya tonu: An cirewa wani Fasto zani a kasuwa



Tonon silili: Wani babban Limami ya shiga uku



Asirin wani sanannen Fasto ya tonu bayan da aka samu labarin cewa ya yaudari wata Budurwa da yi mata karyar zai aure ta. Faston dai ya taba kira da a kashe makiyaya Fulani duk inda aka gan su a kusa da harabar sa.

Fasto Johnson Sulaiman Limamin cocin nan na ‘Omega Fire’ yana cikin tsaka mai wuya bayan da aka kama sa yana alaka da wata Budurwa Stephanie Otobo wanda ta ke karar sa a kotu bayan ya yaudare ta. 

Yanzu haka dai an kama wannan Budurwa Stephanie Otobo a Legas. Kuma ana shirin fara shari’a ne da ita a wani kotun majistare da ke Garin na Legas. Jaridar nan ta Sahara Reporters ce dai duk tayi wannan aiki.

Budurwar tana karar wannan babban Limami bayan da tace ya yaudare ta inda yayi mata karyar zai aure ta ya rika lalata da ita. Faston dai ya taba cewa a kashe makiyaya Fulani duk inda aka gan su a kusa da harabar sa har ta kai Jami’an DSS sun yi ram da shi. 



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...