Saturday, March 11, 2017

HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN



HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA







Dawowar Shugaba Buhari-Daga Bakin Imam Dr. Saeed Muhammad Yunus


Assalamu Alaikum wa Rahmatul Lah,
Dukkan Godiya sun tabbata ga Allah SWT mai ni’ima mai falala wanda ke daga wanda ya so ya kuma sauke wanda ya so. Muna shaidawa bai da ‘da ko mata ko tamka ko wani abokin tarayya. Mun kuma shaida shi ya aiko Annabi Muhammad SAW a matsayin Shugaba. Muna gode masa da gaisuwa gare sa.

Bayan haka:
‘Yan uwa mu ji tsoron Allah mu kuma gode masa, muyi da’a gare sa mu kuma nisanci munanan ayyuka. Mu sanya katanga ko ginshiki da zai kare mu daga azabar Allah. Mu godewa Allah da ya saka mana ni’ima ta Musulunci da lafiya da kuma ni’imar ganin ayoyi; daga ciki mun ga cewa Allah SWT shi ke dagawa kuma shi ke saukeawa. Allah SWT shi ke gudanar da rayukan dabbobi har da kwari. Saboda haka in dai ni’ima ce ba za mu iya kididdige yawan su ba kamar yadda Allah SWT ya fada mana.

Wata Juma’a ce sabuwa ga ‘Yan Najeriya wanda ta cacanci ayi mata huduba ta musamman saboda Allah SWT ya dawo mana da wani wanda muke so-wanda Allah ne ya sa mana son sa. Na rantse da Allah ba shi bane ya sa mana son sa, Allah ne ya sa mana son na shi. Don Allah yace da Manzon Allah cewa: ‘Allah ne ya karfafe ka da nasara ya kuma hada ka Muminai wanda suke taimakon ka… Amma yanzu idan da za ka ciyar da duk abin da ke Duniya, ba za a so ka ba.’ Yanzu idan ka isa ka taba mutuncin Manzon Allah SWT sai ka ga mutane wadanda ba su san Manzon Allah ba ko ya za suyi maka. Haka ne Allah SWT ya sakawa Jama’a son Muhammadu Buhari a Najeriya. Wannan ko kana so, ko kana ki sai dai kayi hakuri kurum, don haka Allah yake zaben bawa daga cikin bayin Sa yace a so shi. Ubangiji ne ya sa Jama’a ke kaunar Muhammadu Buhari ba ko kudi ya ba mutane ba, wani yana rike da kudi fiye da na sa. Wani yana da dangantaka wanda ta fi tasa. Kai wani ya kasance yana da iko da makamai a lokacin da shi Buhari ba shi da su, amma Allah SWT ya daga sa.

Saboda haka ‘Yan uwa mu natsu! Mu lura da ayoyi  na Allah. Ubangiji ya fada mana cewa Allah zai ta nuna maku ayoyi ya ga ko a wane za ku yi musu. Allah SWT yana cewa za mu yi ta nuna masu ayoyi a nan da can har ga ma kawunan su. ‘Yan uwa kasa ta cika da zalunci da kama-karya irin na zamanin jahiliyya da Manzon Allah SAW ya gada; an tsiri Manzon Allah SAW ne a lokacin da ake shan giya ake cin naman alade, ana kashe mata ana karbe dukiyar Jama’a. Sai ga Annabi SAW kuma har bayan Manzon Allah aka yi ta samun Halifofin sa da wanda su ka biyo baya.

Jama’a idan muka duba abin da ya rika faruwa a Najeriya za mu ga yadda tarbiyya ta lalace; babu babba babu yaro. Ga Sarakuna iyayen kasa da manyan Malamai a Garuruwa, duk sun zama ba su da wani daraja ko kadan. Kasar mu ta kasance mun zama ba mu da tsari ko sahu. Kasar nan ta zama cewa komai yadda ka rufe kofar gidan ka wani na iya fado maka cikin dare yayi maka barna. Mun wayi gari a wannan kasar wasu za su tare ka suyi maka fashi ko wani ya banke ka ya tsere. Wannan fa abin da yake waje kenan, idan ka shiga cikin gidaje za ka ga yadda ake zaluntar iyaye mata da su ma yadda suke zaluntar mazajen su ta hanyoyi da dama. Ka leka Ofisoshi za ka ga yadda Ma’aikatan Gwamnati suka zama manyan barayi sannan kuma ga wasu da ake kira ‘Malamai’ da suke yi masu fatawa cewa su diba kudin ba komai ga hakan ko da cewa akwai hadisin Manzon Allah SWT da ke cewa: Wadansu mutane suna kutsawa cikin dukiyar Allah mai girma ba tare da hakkin su ba, Ubangiji SWT kuma yana kallon su, Manzon Allah yace wadannan mutane a ranar lahira ‘yan wuta ne. Dukiyar Najeriya ta kasance na wasu mutane ne da suke rabawa tsakanin su. Ina rantse maku da Allah babu wanda ya tsira daga wannan; har ta kai wani yana izgili yana fada cewa duk wanda ya fito masa da rana sai yayi shanya!

Wannan abin bakin ciki ne da aka dade ana yi a Najeriya kwatsam sai ga wata rana da aka yi zabe a Najeriya, a wannan karo kuri’a tayi tasiri yayin da talakawa su ka yi zabe. Tun da dai an yarda da wannan tsari na Damukaradiyya wanda Musulunci yace ayi tayi muddin ba za a hana Musulmi ibadar sa ba. Sai ga Allah SWT ya daga wani wai shi Muhammadu Buhari a Najeriya. Amma abin da zai ba ka mamaki shi ne akwai Makiya ciki da waje, masu kin wannan gyara da ake so ayi domin Jama’a su samu aminci. A zamanuin Sarki Umaru dan Abdulazeez ya kasance sai kere-keci ta hadu da akuya tayi mata sallama, haka ake fata cewa a sa mu dawwama kowa kuma ya ji dadi! Abin ban sha’awa dai Addinin musulunci bai hana Shugaba ya taimakawa wanda ba Musulmi ba, mu duba yadda Annabi SAW yayi mu’umala da Yahudawa har wasu suka musulunta. Dama dai ba fatan mu kowa ya musulunta ba don kuwa an fadawa Annabi SAW sau da dama a Kur’ani cewa: Za ka tilastawa mutane su zama musulmi? Ba za ka iya ba…’ Ubangiji bai daurawa Jama’a wannan ba. Lalata ta shiga har cikin Malamai masu ‘taimako’ wanda da su ake yin wannan badakalar. Akwai mata mazinata da mashaya giya mai tsada, sace-sace da barna sun cika Kasar nan. Abin bakin ciki sai dai wasu abin da suke so shi ne a cigaba da wannan aiki. Ku duba fa ko an yi maganar gyara a yanzu sai kace har yanzu kadan aka gyara don kuwa an tauna tsakuwa ne sai aya ta firgita. Idan har muna da hankali za mu iya tuna abubuwa da suka faru baya.



Wata sabuwar Juma’a ce ga ‘Yan Najeriya da Allah mai girma ya nunawa aya. Saboda haka ‘yan uwa ku ji tsoron Allah cikin maganganun ku sannan ku kiyayi Allah SWT. Wasu maganganun ku da kare-karen za su zame maku bala’i a Ranar Lahira. Wallahi za ku shiga uku a gobe kiyama!

‘Yan uwa ku tuna abin da ya faru a baya Inji Huduba, mu tuna abin da ya faru a baya; ya kasance fitowa daga Sabon Gari ko cikin Zariya zuwa Jami’ar Ahmadu Bello da ke Samaru ya zama tashin hankali, kullum sai an yi wa iyali wasiyya. Idan kuma har ka je inda abin yake faruwa, to babu yaro kuma babu babba. Mutane suna cikin damuwa babu mai taimako; an kama samari an yanka kamar rago, kananan yara kuma an kashe su kamar kiyashi, ba a tausayin tsoho idan ya nemi ya wuce gona da iri. Daga ana kokarin zuba ruwa sai ka ga wata wutar fitinar ta taso. Har aka samu wannan yanayi, Idan ba ka sani ba, ka nemi a ba ka labari.

‘Yan uwa huduba tana ce mana ina wadanda suka ce Ai Buhari ba zai dawo ba? To Allah ya dawo da shi. Al-Kur’ani ya fada mana yadda wasu suka yi alkwari cewa za su yi imani idan har wata ya tsage kuma bayan wata ya tsage kamar yadda su ka nema, sai kuma ba su yi imani ba. Haka mutanen Annabi Salihu AS suka nemi Allah SWT ya fito da Taguwa daga kurman dutse, Annabi Salihu ya roki Allah kuma taguwar ta fito, amma sai su ka soke ta! To ku ‘Yan Najeriya da ku ka ce za ku musulunta idan har Buhari ya dawo, to muna jiran ku da musulunta, idan akwai wasu a cikin wannnan masallaci sai ku zo ku karba Musulunci, ga ni ina nan kan mimbari, idan kuma kuna jin kunya sai ku tafi masallacin Unguwa ku musulunta.

Allah ya cika alkawarin sa! Malamai za su fada maku cewa Allah Mai Girma ba ya son wuce gona da iri; wani ya bugi kirji yace sai abu kaza ya faru da wane. Wani ya taba cewa ga wani zai shiga wuta, sai Allah SWT ya aika masa cewa ya yafewa wancan, kuma shi ne zai shiga wuta. Duk matsayin ka da Allah ba ka isa ka ce da wani ba zai shiryu ba; Dubi yadda Manzon Allah ya rika ambaton wadanda suka kashe masa Sahabai a Sallah yana tsine masu, sai Allah SWT ya saukar da aya a Al-kur’ani.

Jama’a menene abin gaggawa idan har wannan Dattijo ya rasu? Manzon Allah Muhammadu SAW ya cika, Allah ya fadawa al’umma cewa idan har Annabi ya bar Duniya shin za ku bar Addini? Shin daga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya rasu kuma sai a bar gyara a Najeriya? Ai kuwa da mun shiga uku idan har babu wani irin sa mai gyara a Najeriya. Idan har mu Musulmai ne na kwarai sai mu fara gyara halayen mu, mu nemi tarihin Buhari tun kafin ya rasu.

Ni dai na ga lokacin da shugaban kasa ya sauko daga jirgi ya kuma zarce Abuja. Ina maku haduba cewa ga sako nan na wuce gona da iri da wasu ke yi. An matsu a wancan lokacin Manzon Allah SAW ya rasu, Allah Mai Girma yace idan har Annabi SAW ya rassu shin su za su dawwama ne? Duk mai rai mamaci ne. Wata rana Sayyidina Umar RA yayi huduba yace kowa ya shiryawa mutuwa. Can wata rana kuma dan sa Abdullahi dan Umar RA sai yace dukkan mu nan matattu ne! Don haka ina kara fada cewa dukkan mu nan matattu ne. Wasu daga cikin wadanda su ke wannan magana yanzu sun riga Shugaban kasar rasuwa. An ce dama mutuwa gida ne da kowa sai ya shiga don haka huduba na fada mana cewa mu yi hankali da bakunan mu domin za ayi mummunar azaba ga harshe a gobe kiyama. Annabi SAW ya fadawa Sahabi Abu Hurayrah AS ya kiyaye harshen sa. Haka kuma Jama’a su guji wuce gona da iri wajen murna kar mu zama kamar Mahaukata. Mu roki Allah ya taimaki kasar nan da ‘Yan Jam’iyyar Buhari da wadanda ba su ba.

Allah ya taimake mu ya karawa Buhari lafiya ya sa ya zama tsani domin gyaran Kasar nan. Allah duk wani mai kunci ka yaye mas aka azurta Buhari da Mashawarta ka kare sa daga Munafukai. Allah ka shiryar da lalatattu kar ka sa mu lalace. Ameen. 




Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Masallacin I.T.N-Zaria.
Muhammadmalumfashi@gmail.com          
Twitter: @Ya_waliyyi



No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...