Ka san nawa ne farashin Dala
a Yau?
Bayan dogon lokaci dai
darajar Naira na ta kara sama tun daga sama da N500 har zuwa N360 NAIJ.com na
samun labari cewa yanzu kuma farashin dalar ya dan kara tashi
Farashin dala ya kara tashi bayan an dauki dogon
lokaci dalar na yin kasa. An dai dauki kusan wata guda darajar dalar in ban da
kasa kurum ba abin da yake yi. Da sai da darajar Dalar ya haura N500.
Sai dai daga jiya zuwa yau Naira ce ta sha kasa a
kasuwar Duniya inda ta yi kasa a kan Dala daga kan N382 zuwa N385. Dalar Pounds
ta Ingila kuwa dai ta kai N400 yanzu a kasuwar ‘yan canji kamar yadda NAIJ.com ke samun labari.
Cikin wata guda kawo yanzu dai dala tayi wani mugun
kifewa daga sama da N500 zuwa N360 a bankuna kwanakin baya kamar yadda muka
rahoto. A wannan makon ne bankin kasar watau CBN ya bada umarni bankuna su rika
sayarda dala a kan N360.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa
tattalin arzikin kasar nan dai na murmurewa bayan ya ruguje a baya. Da alamu
dai abubuwa sun dan fara mikewa a Najeriya.
No comments:
Post a Comment