– Ministan sufuri yace bai dace Gwamnoni suyi kokarin hana Achaba ba
–
Rotimi Amaechi yace hana ‘Achaba’ zai kawo babbar
matsala a Najeriya
– Gwamnoni
dai na kokarin hana hawa babur da keke
napep
Ministan sufuri na kasa
Rotimi Amaechi yace
bai dace Gwamnoni suyi kokarin hana Achaba ba. Amaechi yace hakan zai kawo
matsala ne kurum ga tattalin arzikin kasar don haka ya gargadi Gwamnonin kasar
da wannan kudiri.
Rotimi Amaechi ya
bayyana haka ne ga hukumar dillacin labarai watau NAN wajen taron kungiyar masu
‘keke napep’ da babur na kasa. Amaechi yayi wa Gwamnoni kashedi cewa kul aka
hana Jama’a hawa achaba domin zai kara radadin da ake ciki na tattalin arziki.
Ministan yace abin da
ya kamata ayi shi ne a koyawa ‘yan achaban da sauran matuka aiki da bin dokar
hanya saboda irin yawan haduran da ake samu a a fadin kasar. Amaechi yace masu
babur suna da amfani don kuwa ba ko ina mota ke iya ratsawa ba.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment