– Shugaban Kasar Amurka ya kara kawo wata doka da za ta hana ‘yan wasu kasashe shiga kasar Amurka
– Kasashen da ake shirin haramtawa
shiga Amurka dai duk na Musulmai ne
– A
baya dai Trump yayi ta gamuwa da tasgaro
A jiya Litinin ne shugaba Donald Trump na Amurka ya
sanya hannu a wata doka da za ta hana wasu ‘yan kasashen Musulmai shigowa cikin
kasar Amurka. A baya dai shugaban kasa Donald Trump yayi wannan yunkuri sai dai
ya gamu da cikas daga kotun kasar.
A dokar za a hana bada takardan shiga Amurka ga wasu
kasashe wanda na Musulmai ne. Kasashen dai sune: Libiya, Siriya, Iran,
Somaliya, Sudan da kuma kasar Yemen. Sai dai wannan karo an cire kasar Iraki
daga jerin kasashen.
Haka kuma kasar Amurka za ta dakatar da shirin ta na
karbar baki na watanni biyu. Kuma dai Trump ya rage yawan ‘yan gudun hijiran da
ke iya shigowa Amurka daga fiye da 110, 000 zuwa 50,000 kacal a shekara. Ana
dai sa ran wannan doka ba za ta gamu da wani tasgaro ba.
A baya dai shugaba Donald Trump ya hana Kasashe 6
shiga Amurka na watanni hudu yayin da ya kuma ya haramtawa ‘Yan Kasar Siriya
shigowa Amurkar har abada. Wata Kotu da ke Brooklyn ce ta hana a dabbaga wannan
doka ta sabon shugaban Kasa.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment