Ashe wani babban Sanata bai
kammala makaranta ba?
Jaridar Sahara Reporters ta
tasa wani Sanata a gaba inda tace ashe bai kammala Jami’ar ba. Sai dai Sanatan
ya maida martani yace ayi a gaji a kyale sa
Jaridar Sahara Reporters ta bayyana cewa Sanata Dino
Melaye bai karasa karatu a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya ba aka sallame sa.
Sahara Reporters ta fitar da hotunan kwas-kwasan da Sanatan ya dauka inda aka
nuna cewa ya fadi.
Sanatan ya mayar da martani inda yace sharri ne kurum
ake masa. Melaye yace nan gaba ma ana iya cewa shi ba ‘Dan Najeriya bane.
Sanata Melaye yace ba wannan bane karo na farko da Sahara Reporters tayi masa
sharri.
Dino Melaye ya bayyana cewa yanzu haka yana karatu a
Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariyar inda yake Digirin sa na 7. Sanatan yace a je a
duba idan har karya ne a sa Magu na EFCC ya kama sa ya daure.
No comments:
Post a Comment