– A
wannan hali Najeriya na fama da durkushewar tattalin arziki
–
Sai dai da alamu abubuwa za su yi kyau dan nan gaba
– Alkaluma
su na bayyana cewa Najeriya na farfadowa
A halin yanzu dai
Najeriya na cikin matshi na tattalin arziki sai dai yanzu abubuwan kyau suke
karawa ba tabarbarewa ba idan muka yi la’akari da wasu abubuwa da dama. Tattalin
arzikin Najeriya dai ya rugurguje a bara.
Jiya aka bayyana cewa
an fara samun sauki wajen hauhawar farashin kaya wanda a da can dai kullum
cikin tashi suke. Haka kuma jiimilar kudin kasar watau GDP yana ta kara yawa ne
kamar yadda nazari ya nuna.
Yanzu haka dai kudin
gangar mai ya tashi don haka Najeriya na kara samun kudin shiga baya ga cewa
kuma an samu sauki a Yankin Neja-Delta daga tsageru masu fasa butatan mai.
Wannan ya bada dama kasar ta samu rarar daloli har ake saidawa bankuna. Yanzu
dai asusun kasar waje na kasar kara yawa kurum yake yi.
Kungiyar OPEC na
kasashen Duniya masu fita da mai ta bayyana cewa Najeriya tana cikin sahun
kasashen da yawan man da suke hakowa ya kara yawa a watan Jiya watau Fubrairu.
Yanzu dai Najeriya na hako sama da ganga miliyan 1.6.
Buhari ya gana da Gwamnan CBN jiya
Muna da labari cewa darajar
Naira ya karu a farkon makon nan a kan kusa kowane kudin kasar waje. Nairar dai
ta kara daraja akan Dalar Amurka da kuma Pounds Sterling na Ingila da kuma
Dalar EURO ta kasashen Turai.
Har wa yau Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari tayi abin da zai sa
Ma’aikatan N-Power murmushi inda ta amice da karin N4500 a albashin kowane
Ma’aikaci. An kara wannan kudi ne saboda Ma’aikatan su samu daman sayen na’urar
da za ta taimaka wasu wajen aiki.
No comments:
Post a Comment