Kwanaki aka yi ta faman yada cewa
tsohon shugaban kasa Yakubu Gowon ya samu cikawa. Ga dai Yakubu Gowon din ya
fito da kan sa inda ya bada labarin yadda suka rike Najeriya a baya.
Tsohon
shugaban kasa Janar Yakubu Gowon ya bayyana yadda Marigayi Obafemi Awolowo ya
hana Najeriya wargajewa a lokacin yakin basasa na Biyafara. Gowon ya bayyana
haka ne a Ranar tunawa da Marigayi Awolowo.
A
taron dai Gawon yace bai taba furta cewa kasar Najeriya tana da kudi har ta
rasa abin da za tayi da su ba a lokacin yana shugabanci. An dai dade ana yawo
da wannan maganar da sunan tsohon shugaba Yakubu Gowon din.
Gowon
yace idan da su Awolowo za su tashi daga kabari ba za su ji dadin ganin yadda
Najeriya ta zama ba. Kwanan nan shugaba Buhari ya kira Yakubu Gowon din inda
yayi masa ta’aziyar rasuwar kanwar sa Martha Kande Audu wanda ta cika kwanakin
baya.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment