Kocin
Kungiyar Arsenal Arsene Wenger na kara gamuwa da cikas musamman daga magoya
bayan Kungiyar ta Arsenal bayan ya kara shan kashi a karshen wannan makon.
Magoya bayan Kungiyar
Arsenal da dama sun fara kiran dole fa Koci Arsene Wenger ya tattara ya san
nayi. Masu goyon bayan Kungiyar sun ce tabbas sun gaji da Wenger don haka ya
dace kurum ya bar Kulob din.
A jiya ne Arsenal ta sha
mugun kashi hannun Kungiyar Liverpool da ci 3-1, wanda wannan dai na iya kawo
masu cikas a kakar wannan shekarar. Magoya bayan Arsenal suka ce duk laifin
Arsene Wenger ne ya ja aka lallasa Kulob din haka har gida da waje.
A wasan dai Wenger ya ajiye
babban dan wasa Alexis Sanchez a benci inda ake tunanin saboda wata takaddama
da suka samu ne a wasan su da Bayern Munich
makonnin baya. Dan wasa Mane na Liverpool dai ya koyawa Arsenal din hankali.
Dama
can Kocin Kungiyar Arsenal watau Arsene Wenger na fuskantar barazana tun bayan
da Kungiyar sa ta kwashi kashin ta a hannun Bayern Munich. Kungiyar Bayern
Munich din dai ta koyawa Arsenal darasi da ci 5-1 a Gasar Champions League. Har
an fara tunanin cewa Kocin Juventus Massimiliano Allegri zai karbe wurin
Wenger.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment