Mutane 3 da suka fi kowa kudi duk Najeriya
– Alhaji
Aliko Dangote shi ne mai kudin Najeriya da ma Afrika gaba daya
–
Mike Adenuga ne ke bayan Dangote a kasar nan
– Ko
kana da labarin wata mata Folorunsho Alakija?
1.
Aliko Dangote
Rahotanni da ke fitowa na
wannan shekarar daga Mujallar Forbes sun nuna cewa Alhaji Aliko Dangote ya fita
daga cikin sahun mutane 100 da suka fi kowa kudi a Duniya. Amma duk da haka
shekara 6 kenan dai har yanzu babu wanda ya kai Aliko Dangote dukiya a kaf
Nahiyar Afrika ba ma Najeriya ba. Dangote ya ba Dala Biliyan 12 baya.
2.
Mike Adenuga
Adenuga ne mai rike da
kamfanin GLO kuma shi ne na biyu a bayan Dangote in dai kudi ake magana a
Najeriya. Adenuga mai shekaru 63 ya mallaki sama da Dala Biliyan 5.8. Adenuga
ne dai na 250 a cikin masu kudin Duniya.
3.
Folorunsho Alakija
Ina ka baro Folorunsho
Alakija? Ka ji manyan mata! Ba ma Najeriya ba, duk Duniya da wuya a samu bakar
mace da ta kera Alakija kudi. Shekarun baya dai ta zarce Attaajira Oprah
Wimfrey ta Amurka. Alakija mai shekaru 66 ta tsunduma ne a harkar mai ta kuma
mallaki sama da Dala Biliyan guda.
[NAIJ Hausa]
Nice
ReplyDeletebadamasibabangida