Boko Haram: Miliyoyin Jama’a na fama
da rashin ruwan sha
A dalilin rikicin Boko Haram
Miliyoyin Jama’a na fama da rashin ruwan da za su sha a Yankin Arewa maso gabas
kamar yadda NAIJ.com ta samu labari
A wani nazari da aka yi an gano cewa kusan mutane miliyan 4
ke fama cikin rashin ruwa a yankin da Boko Haram su ka yi ta’adi. Boko Haram
dai sun barnata kashi 75% na hanyoyin ruwa a Yankin na Arewa maso gabas.
Rikicin Boko Haram dai ya bar dinbin miliyoyin Jama’a babu
ruwan sha Inji Kungiyar UNICEF. Kungiyar mai kula da kananan yara tace a Jihar
Borno ‘Yan Boko Haram sun gama bata duk wasu hanyoyin samun ruwan sha a Garin.
Karancin ruwan sha da kazanta da rashin lafiya na nema ya
zama wani karin tashin hankali a Yankin kasar kamar dai yadda yake faruwa a
kasashen Somaliya, Yemen da kuma Kudancin Sudan Inji UNICEF.
Karancin ruwan sha mai tsabta dai na haifar da cututtuka da
dama musamman ga yaro karami. Boko Haram dai ba karamar barna su ka yi musamman
a Yankin ba inda aka kashe miliyoyi yayin da wasu kuma su ka tsere.
Kwamishinan
lafiya na Jihar Sokoto Dr. Balarabe Kakale ya bayyana cewa cutar sankarau kuma
na cigaba da kashe mutane a Jihar Sokoto. Yanzu haka dai annobar na ta kara
kamari inda ta ga bayan mutane 21.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment