– Uwargidar sabon Gwamna Jihar Ondo Misis Akerodolu tace ba kudi ta bi
lokacin da ta ga mijin na ta
– Misis Akeredolu tace ta hadu ne
da Mijin na ta lokacin suna aikin bautar kasa
– Uwargidar Gwamna Akerodolu tace
tana ganin dan saurayi tace wannan da shi za ayi
Uwargidar
Rotimi Akeredolu wanda aka rantsar a matsayin sabon Gwamnan Jihar Ondo ta
bayyana yadda suka hadu da mai gidan ta a wata hira da tayi. Misis Akeredolu
tace ba wai kudi ta tsaya bi ba a lokacin da Rotimi Akeredolu ya fara neman ta.
Ko
da yake dai ba Bayarabiya bace amma soyayya ya shiga tsakani lokacin da suke
aikin hidimar kasa a Garin Enugu. Matar Gwamnan tace tana ganin sa a wancan
lokaci ta fadawa kawayen ta cewa ta fa samu mijin aure.
Misis
Betty Akeredolu dai Inyamura ce, sun kuma samu haihuwar ‘ya ‘ya har 4 da
Gwamnan. Misis Akeredolu tayi fama da cutar nan ta ‘cancer’ na mama a baya.
Tuni yanzu ta murmure, har ta bude Kungiya mai kula da irin wannan cuta.
Betty
Akeredolu wanda yanzu tana da jika tace Mijin na ta mutum ne mai saukin kai
kuma mai koshin lafiya. Sannan kuma Uwargidan Gwamnan ta bada shawara kuma ga
ma’aurata.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment