Wani Fursuna yayi Digir-gir daga gidan yari; yana shirin komawa yayi Digir-digir
Farfesa Abdallah Uba Adamu
Fursunoni ma suna karatu a Najeriya kamar yadda
shugaban Jami’ar NOUN Farfesa Abdallah Uba Adamu ya bayyana Ranar Litinin
dinnan
Shugaban Jami’ar NOUN wanda ake karatu daga gida ya bayyana
cewa wannan karo har da wani Fursuna ke shirin shiga karatun domin yayi Digirin
sa na uku. Farfesa Abdalla Uba Adamu ya bayyana wannan a Abuja a wajen taron
shugabannin Jami’o’i.
Gidan yari a Najeriya
Shugaban Jami’ar ta NOUN Farfesa Uba ya bayyana cewa Jami’ar
su ce kadai ta ke da cibiya har a gidan yari. Farfesan ke cewa duk wani dan
kason da ke sha’awar karatu sai yayi rajista kurum ya fara daukar darasi.
Farfesa Abdalla Uba Adamu ya bayyana cewa yanzu haka akwai
wanda ya kammala digirin san a biyu watau Masters
yana kuma shirin fara na uku kenan watau PhD kuma duk a cikin gidan yari a
daure. NOUN dai tana dauke da dalibai sama da 200, 0000 daga fadin kasar.
Jami'ar NOUN ta Najeriya
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment