A yau ne tsohon shugaban
kasar nan Cif Olusegun Mathew Aremu O. Obasanjo ya cika shekaru 80 da haihuwa. Ko
da yake dai tsohon shugaban kasar yace bai ma san ranar da aka haife sa ba.
An haifi Olusegun Obasanjo shekaru 80 da suka wuce a
Jihar Ogun, ta kai dai babu wanda ya mulki Najeriya na tsawon lokacin kamar
tsohon shugaba Obansajo. Cif Obasanjo da shugaba Buhari ne kadai suka mulki Najeriya
a zamanin Soji da kuma farar hula a tarihin kasar.
Obasanjo wanda Injiniya ne na Sojoji ya mulki kasar
nan daga shekarar 1976 bayan an kashe Janar Murtala Muhammad zuwa shekarar
1979. A watan Oktoban 1979 ne Obasanjo ya mikawa Alhaji Shehu Shagari mulki
bayan an yi zaben farar hula. Kusan dai ba a taba yin wannan abu a tarihin
Afrika ta yamma ba a wancan lokaci. Hakan ta sa har ya kusa samun kujerar
Majalisar dinkin Duniya.
An so Obasanjo ya karbi mulkin rikon kwarya a karshen
mulkin Babangida wanda hakan bai yiwu ba; ta kai aka mikawa Cif Ernest Shonekna.
Sai dai kuma a lokacin mulkin Janar Sani Abacha, an kama Janar Obasanjo an rufe
da laifin kokarin kifar da Gwamnatin Sojin Janar Sani Abacha.
Bayan rasuwar Abacha ne dai Obasanjo ya fito daga
gidan yari inda ya tsaya takara a
karkashin Jam’iyyar PDP ya kuma yi nasara. Obasanjo yayi shekaru takwas a jere
yana mulki har ma yayi kokarin ya kara zarcewa na gaba wanda dokar kasa ta taka
masa burki.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment