– Gwamnoni sun ce ba za su bar
aikin su ba domin zuwa ganin shugaba Buhari
– Gwamnonin suka ce babu dalilin
yin haka domin kowa ta kan sa yake
– Abdulazeez Yari ya bayyana haka a
jiya
Shugaban
Gwamnonin Najeriya Abdulazeez Yari ya bayyana cewa Gwamnonin Najeriya ba su da
wani shiri na zuwa duba shugaba Muhammadu Buhari da ke Landan. Yari yace babu
wani dalilin yin hakan.
Shugaba
Buhari dai yana Landan tun tsakiyar watan Junairu inda yace zai yi kwanaki 10
rak, sai ga shi dai ya buge har yanzu bai dawo ba. shugaban Gwamnonin Najeriya
Abdulazeez Yari yace babu wani shiri da Gwamnoni suke yi na zuwa duba shugaban
kasar.
Yari
yace Gwamnoni ba za su iya barin aikin da ke gaban su duk su taru a Landan
domin duba shugaba Buhari ba. Yari yace mafi yawan Gwamnonin sun yi waya da
shugaban kasar har da shi don haka babu dalilin tafiya har inda yake domin yana
samun sauki
Gwamnan
yace ba abin mamaki bane don shugaba Buhari ya kwanta rashin lafiya inda aka
duba shekarun sa da kuma ayyukan da ke gaban sa. Gwamnan yace sai dai ‘Yan
Najeriya na ta kokarin yi wa shugaban na su addu’a.
No comments:
Post a Comment