Wednesday, March 8, 2017

Arsenal ta kara shan dan banzan kashi


Gasar UCL: Arsenal ta sha jibga, Madrid tayi gaba




Kungiyar Bayern Munich ta kara ladabtar da Arsenal a gasar zakarun nahiyar Turai. Bayern Munich dai ta kuma zubawa Arsenal ci 5-1 kamar yadda aka tashi a wancan karo a Jamus. Yanzu dai an kora Arsenal daga gasar da kwallaye har 10.

‘Yan wasa Lewandowski da Vidal da Arjen Robben suna cikin wadanda suka leka ragar Arsenal din. Dan wasan Arsenal ya karbi jan kati a wasan yayin da Theo Walcott ya ci wa Arsenal kwallo guda tun da fari.



Haka kuma Napoli ta sha kashi a hannun zakaru Real Madrid da ci 3-1. Shi ma kuma dai haka aka tashi a zagayen farkon kamar wasan Bayern da Arsenal. Real dai tayi waje da Napoli da kwallaye 6-2. Kyaftin Sergio Ramos ne ya jefa kwallaye biyu sai kuma Morata ya kammala aikin bayan dan wasa Mertens ya tsokano mai ‘ya ‘ya.

Shekara 7 kenan ana kora Arsenal daga gasar UEFA Champions League a wannan mataki sai dai wannan karo an yi wa Arsenal din wankin babban bargo.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...