Ministan gona yace babu yunwa a kasar nan ko kusa
Ministan harkar gona da raya
karkara Audu Ogbeh yayi wuf ya karyata rahotannin kungiyoyin Duniya da kafafen
da ke rahoto cewa akwai matsinaciyar yunwa. Audu Ogbeh yace sam ba haka abin
yake ba.
Ministan gona Audu Ogbeh ya karyata bayanan manyan
Kungiyoyoin Duniya har 3 da suka bayyana cewa an kamo hanyar shiga yunwa a
Najeriya. Kungiyar FAO da WFP da kuma IFAD duk na abinci sun ce Najeriya za ta
shiga cikin matsinaciyar yunwa.
Audu Ogbeh ya karyata wannan bincike inda yake cewa
hakan ba zai taba yiwuwa ba don kuwa Najeriya ke ciyar da har sauran kasashen
Afrika ba kan ta kadai ba. Minista Audu Ogbeh yace babu wannan maganar ko kusa.
Ministan yace Kungiyoyin na cakuda yanayin da ake ciki
a bangaren Arewa maso gabas da Boko Haram suka yi barna a matsayin Najeriya
gaba daya. Audu Ogbeh yace ba haka abin yake ba. Ministan yace tun yanzu har
Gwamnati ta kawo takin noma wanda ke da rahusa.
Gwamnatin tarayya na
shirin kawo karshen karancin abinci da ake samu a cikin kasa Inji Mukaddashin
shugaban Farfesa Yemi
Osinbajo kwanaki. A dalilin haka ne aka ware makudan kudi Naira Miliyan 750
domin harkar gona a kasar.
No comments:
Post a Comment