Friday, March 10, 2017

Buhari ya shiga Fadar shugaban kasa






Shugaba Buhari ya gana da Iyalin sa



A yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga Fadar shugaban kasa da ke Aso Villa. Shugaban kasar ya iso filin jirgin sama na Kaduna a Jirgin shugaban kasa, daga nan ya zarce zuwa Birnin Tarayya,  dazu haka shugaban ya shiga Fadar Aso Villa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da iyalin sa; Shugaban kasar ya hadu da Mai dakin sa Hajiya Aisha Buhari da kuma Uwargidar Mataimakin shugaban kasa Misis Dolapo Osinbajo da wasu Jikokin sa.




Na samu sauki Inji Shugaba Buhari

Majiyar mu ta nuna mana cewa an yi wani dan karamin biki domin shigowar shugaban kasar. Mun samu rahoton cewa shugaban kasar ya gana da Ministocin sa a Fadar wanda daga ciki akwai Rotimi Amaechi.

Har wa yau dai mun ji labarin cewa shugaban kasar yace jikin say a murmure, shugaban kasar yace yanzu yana jin kan sa wasai. Tun a inda ya sauka wani Dan Jarida ya tambaye sa ko ya jikin sa, shugaba Buhari ya fada masa cewa ai ga shi nan yana ganin sa.



No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...